Takaddama a kan sunan fadar gwamnatin Ghana

Shugaban Ghana, John Atta Mills
Image caption Shugaban Ghana, John Atta Mills

A kasar Ghana, wata takaddama ta taso tsakanin gwamnatin John Atta Mills da babbar jam'iyar adawa ta NPP, dangane da sauya sunan sabuwar fadar shugaban kasar da gwamnati ta yi, daga Jubilee House zuwa sunanta na asali, wato Flagstaff House.

Tsohuwar gwamnatin John Kufuor ce ta sauya sunan zuwa Jubilee House, don ya dace da cikar kasar shekaru 50 da samun 'yancin kai.

A jiya ne aka ga sunan na Flagstaff House a jikin fadar shugaban kasar.

Tun farko gwamnatin Ghanar ta ki cewa uffan dangane da lamarin.