Nijar ta yi bayani kan tsaro a Agadez

Hukumomin jumhuriyar Nijar sun bada karin haske a kan aikin wani kwamitin hadin gwiwa na tsaro, a tsakanin Majalisar Mulkin sojan kasar da kamfanin AREVA mallakar Faransa.

An dora wa kwamitin alhakin shirya dabarun tunkarar matsalar tsaro, musamman a jihar Agadez.

Daukar wannan mataki ya biyo bayan sace wasu Faransawa biyar ne da yan Afirka guda biyu, wadanda ake zargin yan kungiyar Alqaeda ne suka aikata.

Shugabar kamfanin Areva, Mrs Anne Lauvergeon, tare da gwamnatin Nijar ne suka yanke wannan shawara bayan ziyarar da ta kai kasar a makon jiya.