Henry Okah ya ce an nemi ya bata sunan 'yan arewa

Henry Okah
Image caption Tsugune ba ta kare ba

Mutumin da gidan talabijin na Aljazeera ya ce shi ne tsohon shugaban kungiyar MEND, mai fafutukar kwato 'yancin Niger Delta, Henry Okah, ya zargi gwamnatin Najeriya da yunkurin amfani da shi wajen shafa kashin kaji ga 'yan siyasar arewacin kasar.

Ya ce ana son yin amfani da shi don dora ma ‘yan arewar alhakin kai harin bamabaman da suka yi sanadiyyar rasuwar mutane 12 a ranar juma'ar da ta wuce a Abuja.

A cewar Mr Henry Okah'n, ya yi zargin cewa gwamnatin Nigeria ta umurce shi da ya sa yan kungiyar MEND su janye ikirarinda suka yi cewa su ne suka kai harin.

Aljazeera dai ta ce ta yi hira da shi ne ta wayar salula a yau daga inda yake tsare a gidan kurkuku a kasar Afrika ta kudu.

A hirar, ya shaida ma gidan talabijin din cewa kin bin umarnin gwamnatin Najeriyar ne ya sanya shi cikin halin da yake yanzu.

Kungiyar yakin neman zaben Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta bayyana kalaman tsohon shugaban wani bangare na kungiyar nan da ke ikirarin kwato 'yancin Niger Delta, MEND din, Henry Okah, cewa, yana da ban tsoro.

A wajen wani taron manema labarai da ta kira dazu, kungiyar ta kuma bayyana cewa kame shugabanta da jami'an tsaro na SSS suka yi a jiya bisa zargin cewa yana da hannu a hare-haren na Abuja.

Ta kuma ce, wani mataki ne na sanyawa masu adawa da shugaban kasar takunkumi, al'amarin da suka ce ba zai zama alheri ga dimokuradiyyar kasar ba.

Gwamnatin Najeriya dai ta musanta ikirarin na Henry Okah.