Daurin rai da rai a kan harin bom a New York

Faisal Shahzad
Image caption Ya nuna bai yi nadama ba

An yanke hukuncin daurin rai da rai a kan Ba-Amurken, Faisal Shahzad, nan dan asalin Pakistan, wanda aka zarga da kokarin tada bam a dandalin Times da ke New York.

Faisal Shahzad ya fada gabanin kai harin cewa, “Tun bayan harin 11 ga watan Satumba nake da muradin hade wa da 'yan’uwana masu jihadi, kuma na gode Allah yau ina shirin kai hari a Amurka.”

A watan Mayun shekarar da ta wuce ne Faisal Shahzad, wanda ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa, ya ajiye wata mota makare da bama-bamai a dandalin, to amma bam din ya ki tashi.

Kwana biyu bayan yin hakan ne aka cafke shi a lokacin da yake kokarin shiga jirgi domin barin kasar.

Shahzad ya samu horo ne daga kungiyar Alqaeda a Pakistan, ya kuma shaida ma kotun a New York cewa, ya yi hakan ne domin kare addinin Musulunci.

Y ace yanzu aka fara yakin da Amurka ke yi da Musulmai.