Yan bindiga sun kai hari gidan Kakakin majalisar jihar Borno

Rahotanni daga jihar Borno a Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun kai hari a kofar gidan Kakakin Majalisar Dokokin jihar.

Sun dai budewa dan sandan dake gadin gidan wuta, suka kuma yi awon gaba da bindigarsa.

Wannan kuwa na cikin irin jerin hare-haren sari-ka-noken da yan bindigar suke kaiwa yansanda da masu unguwanni a birnin na Maiduguri a baya bayan nan.

A kusan mako biyun da suka gabata ne wasu yayan Kungiyar nan ta Boko Haram suka fito suka bayyanawa BBC cewar suke da alhakin kai wadannan hare-hare da kuma irin dalilansu na aikata hakan.