An sako yar adawa a Habasha

An sako yar adawa a kasar Habasha
Image caption Hukumomin Habasha sun sako Birtukan Medeksa

An saki wata fitacciyar shugabar yan adawa a Ethiopia daga gidan yari.

An dai daure Birtukan Medeksa ne sau biyu bisa zargin cewa tana da hannu a jerin zanga-zangar da aka yi, bayan zaben shekara ta 2005, wanda aka yi ta takaddama a kai.

Ita ce dai jagorar wani kawancen jam'iyyun adawa a kasar ta Ethiopia, kuma masu sukar lamirin gwamnatin kasar, sun ce gwamnati ta kama ta ne don ta hana ta shiga zabubbukanda aka yi a watan Mayun da ya gabata.

Kahon zukar da aka kafawa 'yan adawar yayi tasiri, domin kuwa a zaben da aka gudanar a Ethiopiar a watan Mayun da ya wuce, jam'iyyar Pirayin Minista Meles Zenawi ta sami babban rinjaye ba tare da wani jibi ba.