Majalisar Dattijan Nijeriya ta yi tir da harin Abuja

Majalisar dattawan Najeriyar ta yi Allah wadai da tagwayen hare haren bama baman da aka kai a Abuja babban birnin tarayyar kasar, lokacin da ake bukukuwan cika shekaru 50 da samun yancin kan kasar a ranar 1 ga watan nan.

Haka kuma a zaman nata na yau, Majalisar ta umurci wasu kwamitocinta da su bincika tare da gabatar mata da rahoton duk abubuwan da suka faru dangane da hare haren.