Matsalar tattalin arziki na damun bakin haure

Image caption Bakon haure

Sakamakon wani bincike da BBC ta yi na nuni da cewa masu yin kaura zuwa wadansu kasashen musamman matasa maza, na da ga cikin wadanda tabarbarewar tattalin arzikin duniya tafi yi wa illa.

Mawallafan rahoton dai sun bayyana cewa sun gano irin yadda masu kaura su ka fi 'yan kasa dandana kudar tabarbarewar tattalin arziki a kasashe da dama acikin shekaru biyun da suka shude.

Rahoton na nuni da cewa, adadin masu kaurar daga matalautan kasashe zuwa attajirai, ya karu a shekarun da suka gabata.

Amma kuma ya yi nuni da cewa, duk da dai mutanen da ke kaura zuwa wasu kasashe domin neman ayyukan yi su ne wadanda matsalar tattalin arzikin ta duniya ta fi shafa, adadin miliyoyin kudaden da suke aika wa iyalansu gida a kowacce shekara kusan za'a ce bai sauya ba.