Ana cikin mummunan yanayi a kasar Haiti

An shiga mummunan yanayi a Haiti
Image caption An shiga mummunan yanayi a Haiti

Wata kungiyar agajin Amurka ta yi matukar sukar lamirin matakanda Majalisar Dinkin Duniya ke dauka na agaza wa wadanda mummunar girgizar kasa ta shafa a Haiti, kusan watanni goma da suka wuce.

Kungiyar, mai suna Refugees International, ta ce wasu kungiyoyin masu aikata miyagun laifukka ne ke tafiyar da sansanonin 'yan gudun hijirar da aka tsugunar da 'yan kasar Haitin da suka rasa muhallansu, kuma yin fyade, da tilasta wa mata bada kansu, domin a ba su abinci ya zamo ruwan dare.

Halinda ake ciki a sansanonin 'yan gudun hijirar da aka kafa, sakamakon girgizar kasar da ta afka ma Haiti, mummuna ne.

Tantunan da ake amfani da su a sanasnonin ba su dace da yanayin kasar inda yanzu haka ake fama da matsanancin zafi da kuma guguwa tare da ruwan sama ba.