NUC ta haramta wasu kwasa kwasai a Jami'o'in Najeriya

Image caption Taswirar Najeriya

Hukumar kula da jami'o'i ta Najeriya, NUC, ta haramtawa wasu jami'o'in kasar ci gaba da koyar da wadansu kwasa kwasai, har sai sun cika sharuddan inganci da hukumar ta zayyana.

Sharuddan sun hada da kamar misali yawan malaman da suke koyar da kowanne kwas a cikin kwasa kwasan da abin ya shafa, da azuzuwan da ake koyar dasu, sannan kuma idan kwas din ya shafi kimiyya, sai dakin gwaje gwajen kwas din ya cancanci a iya amfani dashi wajen koyarwa.

Adadin kwasa kwasan da wannan haramci ya shafa sun kai kimanin dari da sittin da bakwai a jami'o'i arba'in da biyar daga jami'o'i dari da hudu da ke kasar, mallakar gwamnatin tarayya, da na jihohi da kuma masu zaman kansu.

Sanya wannan takunkumi dai na nufin cewa daga shekarar karatu ta badi jami'o'in ba zasu dauki sababbin dalibai a kwasa kwasan da aka dakatar ba.

Amma kuma hukumar ta bada tabbacin cewa wadanda su ke karatunsu yanzu suna da damar kammalawa.