Matsalar rashin tsaro a Najeriya

Rahotanni daga Jihar Borno da ke arewacin Najeriya sun bayyana cewa a daren jiya wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba, sun kai hari gidan Mataimakin Shugaban Jam'iyar ANPP na shiyyar arewa maso gabashin Najeriya Alh Awana Ngala, inda su ka harbe shi har lahira.

Wannan al'amari dai ya faru ne sa'o'i uku bayan harin da wasu 'yan bindigar suka kai gidan shugaban Majalisar Dokokin jihar Borno Alh Goni Ali Modu, a yammacin jiya.

Sun harbe wani dan sanda dake kofar gidansa a bainar jama'a sannan suka yi awon gaba da bindigarsa.

Jami'an tsaro tuni suka bazama wajen bincike domin gano ko su wa ye su ka aikata wannan aika aikar.

A kusan makonni biyun da suka gabata ne dai wasu daga cikin 'ya 'yan Kungiyar nan ta Ahlus Sunnah wal jihad da ake kira Boko Haram suka bayyanawa BBC cewa su ne ke da alhakin kai irin wadannan hare-haren.