Archibishop ya nemi a zauna lafiya a Sudan

Archbishop na Canterbury, Dr Rowan Williams, yayi kira ga kasashen duniya da su kara kaimi wajen tabbatar da cewa ba a sake samun barkewar yakin basasa a kasar Sudan ba.

Al'ummar kasar na cigaba da zaman dar dar a yayin da kudancin kasar ke shirin kada kuri'ar raba gardama, wadda za ta basu 'yancin kai.

A karkashin yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kawo karshen yakin basasar da aka yi a Sudan tsakanin Arewaci da Kudancin kasar, an alkawartawa 'yan kudancin kasar ne cewa za'a kada kuri'ar raba gardamar a watan Junairun badi.

Ana tsammanin samun amincewa akan wannan batu.

Sai dai kuma har yanzu ana fuskantar matsaloli wajen yin rajistar zabe, sannan takaddamar da ake yi a kan iyakoki da kuma yankin dake da arzikin mai a kasar na yiwa wannan kuri'a da za'a kada barazana.

Su dai shugabannin kudancin kasar na zargin na arewa ne da dakile kada kuri'ar, inda kuma suka yi gargadin cewa duk wani jinkiri da aka samu zai iya haddasa yaki.

Wannan batu kuma shine ya tada hankalin Archbishop na Canterbury, wato Dr Rowan Williams.