An bada shawarar sanya dokar ta baci a Zamfara

gubar darma a Zamfara
Image caption An bada shawarar sanya dokar ta baci a Zamfara

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a jahar zamfara da ke bincike kan matsalar gubar darma ta shawarci hukumomin Najeriya da su ayyana jahar ta zamfara a matsayin yankin da masifa ta fada mawa.

Tawagar ta ce ta dauki wannan matsaya ne domin samun tallafin alumomin kasa da kasa wajen tunkarar matsalar.

A cikin rahoton da ta fitar wanda BBC ta samu kwafensa, tawagar tace, akwai dubban mutanenda yanzu haka rayukansu ke cikin hadari saboda gurbatar da ruwan shan al'umomin ya yi da gubar ta darma.

A cikin rahotonda ta mikawa hukumomin Najeriyar da kuma gwamnatin jahar ta zamfara baya ga ziyartar wasu kauyukan biyar, ya nuna cewar, baya ga karuwar mace-macen yara, akwai kuma karuwar kauyukan da ke gurbata da gubar, ga kuma alamun sake dawowa da hakar ma'adinan, a daya daga cikin kauyuka biyun da aka sharewa gubar watau Dareta.