Sabon hafsan hafsoshi a Guinea Bissau

safarar miyagun kwayoyi

Amurka ta bayyana matukar rashin jin dadinta, akan matakin da kasar Guinea Bissau ta dauka na sake mayar da wani da ake zargin cewa shi madugun 'yan safarar miyagun kwayoyi ne, a matsayin babban hafsan mayakan ruwan kasar.

Amurka na zargin Rear-Admiral Jose Americo Bubo Na Tchuto da taka muhimmiyar rawa wajen safarar miyagun kwayoyi a duniya.

Rear Admiral Bubo Na Tchuto dai shine ke jagorantar sojin ruwan Guinea Bissau kafin shekarar 2008, lokacin da aka zarge shi da wani yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Daga nan ne kuma ya yi gudun hijira zuwa Gambia, kafin ya dawo Guinea Bissau a matsayin masunci a bara.

Yanzu kuma Real Admiral din ya bayyana jin dadinsa da afuwar da aka yi masa ta hanyar bashi wannan mukami, sannan kuma ya yi alkawarin tabbatar da daidaito da hadin kai.

Sai dai kuma fadar gwamnatin Amurka dake birnin Washington ta bayyana cewa dawowarsa wani koma baya ne ga kasar.

Ana kuma fargabar cewa kasar za ta ci gaba da fuskantar matsalolin talauci da rashin tsaro muddin shugabanninta basu yanke alaka da masu safarar miyagun kwayoyin dake kasashen yankin Latin Amurka ba.