Liu Xiaobo ya sami kyautar Nobel

An bada kyautar Nobel ta zaman lafiya ta bana ga dan kasar Sin din nan mai nuna bijirewa , Liu Xiaobo.

Kwamitin bada kyautar Nobel ya ce jajircewar da ya dade yana yi, da kuma matakan sulhun da yake dauka na fafutukar da yake yi, su suka sa shi zama wani kyakkyawan abin misali wajen yaki da tauye hakkin jama'a a kasar Sin.

Jonas Gahr Store shi ne ministan harkokin wajen kasdar Norway; Ya ce, Yana cewa ne, kwamitin bada kyautar Nobel ya bada kwararan dalilai na bada kyautar kan abin daya shafi ci gaba da yada dimokradiyya da kare hakin jama'a.

Hukumomin China sun bayyana Liu Xiaobo a matsayin mai aikata laifi, suna masu cewar ba shi kyautar ta saba da manufofin bada kyautar zaman lafiya ta Nobel.