Ra'ayi Riga: Matsalolin wasan kwallon kafa a Nigeria

'Yan wasan Super Eagles
Image caption 'Yan wasan Super Eagles

Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya, watau FIFA ta ce ta jingine dakatarwar da ta yiwa Nigeria har nan zuwa wani lokaci, saboda ta ga alamun an fara aiwatar da sauye sauyen da ta ke bukata.

Wannan mataki zai baiwa Nigeriya damar karawa da kasar Guinea, a wasan kwallon kafa na share fagen gasar cin kofin nahiyar Afrika da zaa yi ranar lahadi.

Hukumar FIFA ta dakatar da Nigeria'r ne daga cikin kungiyar a wannan makon bayan da ta yi zargin gwamnatin Nigeria na yin katsalandam a harkokin wasannin kwallon kafa.

Zargin da hukumar FIFA ta yi ya hada da batun karar da aka shigar a gaban kotu akan zababbun shugabannin hukumar, abun da sam ya hana su gudanar da aikace aikacensu.

Tuni dai aka janye wannan kara aka kuma mayar da Sakatare Janar na riko kan mukaminsa.