Ana zaman zulumi a Borno

'Yansandan Najeriya
Image caption Ana zaman zulumi a Borno

A jihar Borno da ke arewacin Najeriya, jama'a da dama na ci gaba da zaman zullumi sakamakon jerin hare-hare da kashe-kashen da ke ci gaba da faruwa a birnin Maiduguri.

Kimanin mutane goma sha shida ne, wadanda suka hada da jami'an 'yan sanda, 'yan bindiga suka hallaka tun daga ranar biyu ga watan Yulin bana ya zuwa yanzu inda suka bindige wani fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Bashir Mustapha, da almajirinsa Modu, Sunoma, a cikin gidansa.

Hakan na faruwa ne duk da irin matakan tsaron da hukumomin suka fara dauka tun a watannin baya.

Ko a kwanaki ukun da suka gabata sai da 'yan bindigar suka hallaka Mataimakin shugaban Jam'iyar ANPP na kasa shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, Alhaji Awana Ali Ngala, a gidansa, sa'oi uku bayan sun kai hari gidan Kakakin Majalisar Dokokin jihar Borno inda suka harbi dan sandan dake gadin gidan.

Al'ummar jihar sun yi kira ga gwamnati ta dauki matakan gaggawa don magance matsalar tsaro a jihar.