Kim Jong-Un ya bayyana gaban jama'a

Mista Kim Jong-Un
Image caption Kim Jong-Un ya bayyana gaban jama'a

Mutumin da ake kyautata zaton nan gaba kadan zai kasance shugaba kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya bayyana gaban kafafen yada labaru na duniya a karon farko.

Mista Kim ya bayyana ne a bainar jama'a a wani wurin bikin wasanni da raye-raye a Pyongyang, babban birnin kasar, inda ya zauna kusa da mahaifinsa shugaba Kim Jong-il -- wanda ke fama da rashin lafiya

Ana gudanar da bikin wasannin na Arirang a babban birni kasar duk shekara, inda dubban makada da mawaka ke cashewa.

Sai dai a bikin na bana, King Jong-Un ne ya dauki hankalin masu halartar bikin.

Ya bayyana a wajen da ake yin raye-raye na musamman a wajen bikin.

Yana tare da mahaifinsa, shugaban kasar mai ci Kin Jong-Il, wanda ake cewa na fama da rashin lafiya.

Mahalarta bikin wasannin sun kaure da shewa, da tafi a lokacin da aka haska mutanen biyu da wata fitila mai hasken gaske.

An baiwa Kim Jong-Un manyan mukamai guda biyu a gwamnatin kasar, abinda masu sharhi ke gani wata hanya ce ta mika masa jagorancin kasar bayan ba mahaifinsa.