Ziyarar Jonathan ba ta da muhimmanci, inji 'yan adawa

Shugaban Najeriya,Goodluck Jonathan
Image caption An soki ziyarar da Jonathan ya kai Pilato

'Yan adawa a jihar Pilaton Najeriya, sun soki ziyarar da shugaban kasar, Dakta Goodluck Jonathan ya kai jihar.

Sun ce gwamnatin jihar ba ta aiwatar da wasu muhimman ayyukan ci gaba ba,balle shugaban ya kaddamar da su.

Sai dai gwamantin jihar ta musanta wadannan zarge zarge da ta bayyanasu a matsayin adawar siyasa.

Ta kara da cewa ta gudanar da ayyuka da dama, shi ya sa ta ke neman tubarrakin shugaban kasar.