Ghaddafi yayi gargadi kan ballewar kudancin Sudan

Shugaba Ghaddafi
Image caption Shugaba Ghaddafi

Shugaban Libya, Mu'ammar Ghaddafi yayi gargadin cewa idan yankin kudancin Sudan ya zabi samun 'yancin kai, to rarrabuwar kasashen da suke hade zata bazu kwatankwancin cututtuka masu yaduwa a nahiyar Afrika.

Shugaban na Libya yace raba kasar Sudan zai raba taswirar kasar, sannan sauran kasashen Afrika su ma zasu sauya.

Shugaba Ghaddafi yace idan aka bari wannan abu ya yiwu, to za'a ga sauyi a karo na farko kan taswirar Afrika da aka gada. Kuma wannan babban lamari ne wanda yake da hadari.

Kanar Ghaddafi yayi wadannan kalamai ne a taron shugabannin Afrika da na larabawa a birnin Sirte. Shugaba Ghaddafi kuma ya nemi afuwa a maimakon kasashen larabawa kan cinikinn bayi dan daruruwan shekaru.