Majalissar Ministocin Israila ta amince da dokar biyayya

Binyamin Netanyahu
Image caption Binyamin Netanyahu

Majalissar ministocin Israila ta amince da wani shirin doka wanda zai bukaci duk wanda ke bukatar zama dan Israila ya yi rantsuwa ta yin biyayya ga Kasar Yahudawa mai bin tafarkin dimokuradiyya.

Wakilan Larabawan Israila marassa rinjaye, sun nuna rashin amincewarsu da wannan sabuwar doka da ake shirin bullowa da ita.

Mutumin da ya rubuta wannan gyara ga dokokin zama dan kasa na Israila, shine Ministan harkokin wajen Israila mai ra'ayin rikau, Avigdor Lieberman, to amma Firaminista Binyamin Netanyahu, yana goyan bayan wannan shiri.

Idan har Majalissar dokokin Israila ta amince da wannan shiri, to dokar zata tilastawa dukkanin baki wadanda ba Yahudawa ba da suke son zama yan kasar Israila, su yi rantsuwa akan cewar ko sama da kasa zata hade ba zasu ci amanar Israila ba.

A zahiri dai mutane yan kalilanne wadanda ba Yahudawa ba suke gabatar da bukatar zama yan Isaila, kuma wannan doka ba zata yi aiki ba akan dumbin Larabawa yan isra'ilar da suka kai kusan kashi ashirin da biyar cikin dari na yan al'ummar kasar, wadanda kuma tuni dama yan Israila ne.