An fara rarraba katin zabe a jamhuriyar Niger

Salou Djibo
Image caption Salou Djibo

Hukumar zabe mai zaman kanta a Jamhuriyar ta ce ta fara gudanarda ayyukan raraba katunan zabe a fadin kasar baki daya.

Hukumar zaben watau CENI, ta ce mutane kimanin miliyan bakwai ne suka cika sharrudan zabe za su karbi katunansu.

Kamar yadda hukumar ta ce, ba za'a a mince mutane su yi zabe da tsohon kati ba.

Hukumar ta ce ta dauki dukkanin matakan da suka dace domin tabbatar da cewa koya ya karbi katinsa gabanin lokacin da zaa fara zabe a kasar.

Jamaa dai na bukatar wadannan katunan gabanin su samu damar kada kuru'a a kuruar raba gardamar da zaa yi a karshen wanann watan da ma sauran zabubbaka da zaa yi domin mika mulki ga hannun farar hulla.