Shugaban Sudan yayi gargadin barkewar wani yakin

Omar El-Bashir
Image caption Shugaban Sudan, Omar El-Bashir

Shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir ya zargi tsaffin 'yan tawaye na kudancin kasar sabawa ka'idojin dake kunshe a yarjjeniyar sulhun da aka kulla da su.

A karkashin yarjejjeniyar wanzar da zaman lafiyar da aka kulla, akwai sharadin cewar dukkanin bangarorin biyu zasu aiki domin kwadaitarwa da jama'a muhimmancin hada kai.

Haka nan kuma, Shugaba Al-Bashir yayi gargadi akan yiwuwar wani sabon rikicin tsakanin arewacin kasar da kudanci, wanda zai fi na da muni.

Mutane kamar miliyan biyu sune mutu a rikicin na baya.

A watan Janairu ne aka shirya mutanen kudancin kasar ta Sudan zasu kada kuru'a akan yiwuwar samun 'yan cin, a wani bangare na yarjjeniyar sulhun da aka kulla.

Kalaman na shugaba Al-Bashir sun kara ruruta zaman zullumin da ake fama da shi tsakanin yankin Kudancin Kasar da arewaci, a daidai lokacin da kuru'ar raba gardamar ke karatowa.