Zimbabwe na bukatar dala biliyan daya dan inganta fannin lafiya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar Zimbabwe tana bukatar akalla dala biliyan daya domin zubawa a harkar lafiya a kasar daga nan zuwa shekaru uku.

Ana bukatar wadannan kudade domin zuba su harkokin lafiya ga jama'a musamman domin kawar da mutuwar kananan yara sakamakon cututtukan da za a iya kawarwa.

Wakilin Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya a Harare, Dr Peter Salama ya bayyanawa BBC cewa jarirai da dama suna mutuwa saboda iyayensu mata ba su da sukunin zuwa su haihu a asibiti.

Yace mutuwar mata sakamakon haihuwa ya nunka tun 1990.