An soke mukamin sakataren CSRD a Nijar

Janar Salou Djibo, shugaban mulkin sojan Nijar
Image caption Janar Salou Djibo, shugaban mulkin sojan Nijar

Shugaban mulkin sojan Nijar, Janar Salou Djibo, ya rusa mukamin babban sakataren hukumar koli ta mulkin soja, watau CSRD.

Tun bayan juyin mulkin da soja suka yi a ranar 18 ga watan Fabrairu ne aka kafa CSRD, kuma tun daga lokacin ne Kanar Abdoulaye Bague ke rike da mukamin sakataren hukumar.

Kawo yanzu dai sojojin basu bayyana dalilan soke mukamin na sakataren CSRD din ba.

Sai dai tuni wasu kungiyoyin kare hakin bi'ladama irinsu RODDAHD, suka fara yin kira ga sojojin da kada su yi wani abun da zai janyo cikas ga shirin mayar da kasar ta Nijar bisa tafarkin demokradiyya.