Takaddamar musabbabin mutuwar Yar Birtaniya

Linda Norgrove
Image caption Maaikaciyar Birtaniya da ta rasu lokacinda aka yi kokarin kubutar da ita

Kwamandan dakarun sojin Amurka da NATO a Afghanistan, janar David Petraeus, ya bada umarnin gudanar da bincike kan mutuwar ma'aikaciyar bada agaji, 'yar kasar Birtaniyan nan da aka kashe ranar juma'a, a lokacin da ake kokarin ceto ta daga hannun wadanda suka sace ta.

Sanarwar tasa ta zo ne bayan da dakarun sojin Amurka suka bayyana cewa mai yuwa gurnetin da sojojinsu suka harba a lokacin da suke kokarin ceto ma'aikaciyar agajin, Linda Norgrove ne ya kashe ta.

Dakarun sojin Amurkan sun shaidawa BBC cewa hoton bidiyon da aka dauka ta sama ya nuna abubuwa daban daban.

Hasashenda aka yi da farko dai ya nuna cewa, ta rasu ne sakamakon wasu bama bamai da suka tashi wadanda yan bindigar da suka sace ta suka dana.