Mutane biliyan guda na fama da yunwa a duniya

Matsalar abinci a duniya
Image caption Rashin kyawun damuna ya haifar da matasalar abinci a wasu sassa na duniya

Wani sabon rahoto kan mizanin yunwa a duniya ya ce, kimanin mutane biliyan guda ne ke fama da yunwa a sassa dabam dabam na duniya.

Rahoton na bana ya nuna cewa, rashin abinci mai gina jiki da kananan yara ke fama da shi, yana daya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rashin lafiya a tsawon rayuwar mutum, a sassa da dama na duniya.

Duk da cewar yawan mutanen dake fama da matsalar rashin ingantaccen abinci mai gina jiki a duniya sun ragu tsakanin shekarun 1990 da kuma shekara ta 2006.

A 'yan shekarun nan a iya cewar yawan mutanen sun karu bayan da alkaluman shekara ta 2009 suka nuna cewar mutane fiye da biliyan daya ne ke cikin yunwa.

Hakazalika alkaluman baya bayannan na shekarar 2010, sun yi nuni da cewar yawan mutanen za su ragu amma sai dai alkaluman basu kammala ba tukunna. kasashe ashirin da tara mafiyawanci a kudu da hamadar sahara da kuma kudancin Asia suna cikin tsananin yunwa.

Hauhawar farashi

Matsalar hauhawar farashin kayan abinci na duniya da kuma rikicin tattalin arzikin duniya sun kara taimakawa wajen tabarbarewar abubuwa kamar yadda rahotabn yace.

Rahotan ya kuma ce a yanzu haka halin da ake ciki ya fi yin barazana ga yara kanana 'yan kasa da shekaru biyu.

Rashin isasshen abinci mai gina jiki a wannan mataki na yin illa ga ci gaban kwakwalwa, abinda ke janyo lahani mai tsawo ga rayuwar dan adam.

Mawallafan rahotan sun nuna cewar inganta irin abincin da ake baiwa yara kanana zai taimaka wajen rage matsalar yunwa a duniya.

Sun kiyasta cewar za'a iya rage matsalar rashin abinci mai gina jiki tsakanin kananan yara da kusan kashi biyu bisa uku ta hanyar samar da ingataccen shirin kula da lafiya.

Da kuma abinci amma ba wai kawai ga kananan yara ba, hatta su kansu iyaye mata wadanda ke dauke da juna biyu da kuma masu shayarwa. Rage yawan mutanen da ke fama da yunwa zai kuma taimaka wajen bunkasa tattalin arziki.