An kona ofishin 'yan sanda a Maiduguri

Jami'an 'yan sanda a Najeriya
Image caption Daruruwan mutane aka kashe bara lokacin rikicin Boko Haram

An kona wani ofishin 'yan sanda a garin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya, a wani hari da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram da aikatawa.

An jiwa wani dan sanda guda rauni bayan da 'yan bindiga su ka yi harbi a wajen ofishin, kafin daga bisani wasu abubuwa su fashe inda wani dan sanda da wata mata suka samu rauni.

Akalla mutane 16, yawanci jami'an 'yan sanda aka kashe a birnin cikin watanni biyu da suka wuce.

Hare-haren baya-bayan nan dai sun yi sanadiyyar mutuwar tsohon shugaban jam'iyyar ANPP mai mulkin jihar, da kuma wani fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Bashir Mustapha.

Fada tsakanin 'ya'yan kungiyar Boko Haram da jami'an 'yan sanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane a watan Yulin bara.

Image caption Wannan shi ne hari na baya-baya a jerin hare-haren da ake zargin 'yan Boko Haram da kaiwa a Maiduguri

Wakiliyar BBC a Maiduguiri , Bilkisu Babangida ta ce harin ya biyo bayan kisan wani malamin addinin Islama a ranar Asabar. Ana hasashen malamin yana adawa da kungiyar, wacce ke takun-saka da gwamnatin Najeriya da kuma adawa da ilimin zamani.

Wakiliyarmu ta ce harin na ranar Litinin ya faru ne cikin dare.

Yawancin wadanda aka kashe a kwanakinnan, an kashe su ne ta hanyar amfani da baburan okada.

A wani yunkuri na shawo kan lamarin, an hana hayar babur da daddare, amma har yanzu a na ci gaba da kai hare-hare.

Daruruwan 'yan kungiyar Boko Haram ne suka tsere daga gidan yari bayan da aka kai hari a gidan yarin da a ke tsare da su a garin Bauchi.

A bara ne dai aka kashe 'ya'yan kungiyar da dama ciki har da shugabanta Mohammed Yusuf, bayan wani artabu tsakanin kungiyar da jami'an tsaro.

Karin bayani