Ma'aikata na ci gaba da yajin aiki a Faransa

Masu zanga-zanga a Faransa
Image caption Masu zanga-zanga a Faransa

Kungiyoyin kwadago a kasar Faransa za su ci gaba da yajin aiki domin nuna rashin amincewarsu da matakin da Shugaba Nicholas Sarkozy ya dauka na tsuke bakin aljihun gwamnati ta hanyar rage yawan kudin fanshon ma'akatan kasar.

Wannan dai shi ne karo na hudu da masu zanga zanga za su hau kan titunan kasar.

Yajin aikin dai zai shafi harkar sufuri a kasar ciki har da zirga-zirgar jiragen sama, jiragen kasa da kuma motocin safa.

Tuni dai yajin aikin da ake yi a matatun man fetur na kudancin kasar ya sa farashin man diesel tashin gwauron zabi a Turai.

Gwamnatin Faransar dai ta kara yawan mafi karancin shekarun ritaya ne zuwa sittin da biyu ta kuma ce wadanda suka kai shekaru sittin da bakwai kafin su yi ritaya ne za su samu fansho.