An tsaurara matakan tsaro a ziyarar Jornathan

A Nigeria, shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya kai ziyara jahar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar cikin tsauraran matakan tsaro, sakamakon wata barazanar harin bam da aka samu.

Rahotanni sun ce an samu wani sakon wayar salula da aka ce ya fito ne daga kungiyar MEND wadda ke cewar akwai yiwuwar tashin bama-bamai a wurarenda shugaban zai ziyarta, abinda ya sa wasu ke cikin fargaba a yayin ziyarar shugaban.

Ziyarar ta sa ta yini guda ta gudana ba tare da wata matsala ba.

A ziyarar, ya kaddamar da tashar wutar lantarki a jihar ta Zamfara, inda daga bisani ya garzaya jihar Sokoto.