Majalisar Nijeriya na duba bukatar INEC

'Yan majalisar wakilan Najeriya sun sha alwashin tabbatar da cewa, sun yi dukkan gyare-gyaren da suka kamata ga kundin tsarin mulkin kasar da kuma dokar zabe domin biyan bukatar hukumar zabe ta kasa, watau INEC, ta samun karin lokacin kintsawa zaben badi.

Sai dai wasu 'yan majalisar sun ce ba zasu waiwayi bukatar shugaba Goodluck Jonathan ba, ta yin gyara ga wani sashe na dokar zaben da zai baiwa wasu mukarrabansa damar kada kuri'a a zaben fidda 'yan takara.

Dukkan wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da hukumar zabe ke kokawa akan yadda lokaci ke kara kure mata.