Saharawi na neman AU ta taimaka ma ta.

Shugaban Jamhuriyar Saharawi, Muhammed Abdelaziz, yayi kira ga Tarayyar Afirka, AU, da ta tsoma baki wajen ceto al'ummomin yankin daga kuntatawar da ya ke zargin kasar Morocco na musu.

A wani taron ganawa da jama'a a Abuja, shugaban Saharawin ya ce lokaci yayi da kasar Saharawi zata samu 'yancin kai, kamar dai sauran kasashe a nahiyar Afrika.

Jamhuriyar ta Saharawi ita ce kadai ta rage a Afrika da ba ta da 'yancin kai.

Kungiyar kwadago ta kasa a Nijeriya, NLC , ita ma ta nemi Tarayyar Afrika da ta mara baya, wajen ganin burin jamhuriyar ta Saharawai ya cika.