Dubban mutane na zanga zanga a Faransa

Zanga zangar Faransa
Image caption Zanga zangar Faransa

Dubun dubatar jama'a na yin zanga zanga a birane da garuruwan kasar Faransa, domin kokawa da sauye-sauyen da gwamnati ke shirin yiwa tsarin fansho na kasar. Zanga zangar ta haddasa babban cikas wajen zirga-zirgar jiragen sama da na kasa.

Wannan ne karo na ukku da ake gudanar da irin wannan zanga zangar a cikin wata guda.

Kungiyoyin kwadagon suna zanga zangar ce, duk da cewa dukkanin majalisun dokokin kasar ta Faransa guda biyu, tuni suka amince da manyan sauye-sauyenda ake son yi wa tsarin na fansho.