Ana ci gaba da aikin ceto mahakan ma'adinai a Chile

Fitowar Florencio Avalos daga karkashin kasa
Image caption Fitowar Florencio Avalos daga karkashin kasa

Yanzu haka an fito da fiye da kashi daya cikin uku na ma'aikatan hakar ma'adanan nan da suka makale a karkashin kasa sama da watanni biyu a kasar Chile.

Ana ci gaba da aikin ceto mutanen, kusan sa'o'i da dama kenan da suka gabata.

An garzaya da wasu daga cikin mutanen da ka ceto zuwa asibitin dake kusa wato Copiapo.

Da zaran mutum ya fito daga cikin karkashin kasa, sai hankalin yan uwansa da iyalansa ka ga sun kwanta.

Ministan lafiya na kasar Chile, Jaime Manalich ya ce, wadanda aka fito da su kawo yanzu ba su da wata babbar matsala ta bangaren lafiyarsu.

'jinin su ya hau'

Ya ce,"matsalar da suke da ita ba wata babba ba ce, wato jinin su ne ya hau lokacin da ake fitowa dasu, kuma yanzu haka ya dawo dai dai bayan da suka sa mu suka huta".

Shugaban kasar Chile Sebastian Pinera, yace, na yi imanin cewa Chile ta cika alkawarinta ga 'yan kasar Chile, saboda al'ummar Chile sun bayyana sadaukarwarsu ta nuna rashin gazawa da karfin hali. Mun kuduri aniyar samo su, kuma mun yi hakan.

Iyalan mutum na farko da aka fara fitowa da shi cikin ma'aikatan hakar ma'adanan, Florencio Avalos sun karbe shi cikin farin ciki tare da shugaban kasar Chile Sebestian Pinera.

Daga cikin wadanda aka fito da su kawo yanzun sun hada da dan kasar Bolivina, Carlos Mamani, da karamin cikinsu mai shekaru 19 da haihuwa, Jimmy Sanchez, sai kuma wanda yafi kowanne cikinsu shekaru Mario Gomez mai shekaru 63, da Jose Ojeda mai shekaru 56 dake fama da ciwon suga.

To sai dai har yanzu akwai hadari. Daga cikin wadanda suka rage a karkashin kasa, akwai wadanda ba su da koshin lafiya, wadanda ka iya bukatar kulawa ta gaggawa.

To sai dai yadda aikin ceto ke tafiya, ya baiwa iyalan mutanen kwarin gwiwar cewa, komi na tafiya kamar yadda aka tsara.