Mahaka ma'adanai: Shugaban Chile ya yabawa masu aikin ceto

Shugaban kasar Chile, Sebastian Pinera ya yaba wa injiniyoyin dake aikin ceto mahaka ma'adanan nan talatin da uku daga wani ramin hakar ma'adinai da ya rufta.

Ya zuwa yanzu an zakulo mahaka ma'adinan su ashirin da biyu.

Mr Pinera ya ce kasar ta Chile ta nuna wa duniya irin jajircewa, da imaninta da kuma fata.

Shugabannin Chile da Bolivia sun tarbi mutanen da aka fito da su, wanda daya daga cikinsu dan kasar Bolivia ne.

A cewar Evo Morales, shugaban na Bolivia "Lamarin kamar a mafarki, amma kuma da gaske ne. 'Yan Bolivia ba za su taba mantawa da shi ba"