Ahmadinejad na ziyara a Lebanon

Shugaba Mahmud Ahmadinejad na Iran ya yiwa dubun dubatar magoya bayan kungiyar Hezbolla jawabi a birnin Beirut.

Tun da farko Mr Ahmadnejad yace Iran na goyan bayan hadin kan Lebanon dari bisa dari, a matsayin wata hanyar cire fargabar da wasu ke cewa ziyarar tasa na iya yin illa ga siyasar kasar dake da rauni:

Shugaba Ahmadinejad yace: Munyi amanar cewa mutanan Lebanon da ma yankin mu baki daya na iya tafiyar da al-amuransu, su kuma yi mu'amala da juna bisa shari''a da girmamawa, bama yin katsalandan a wasu kasashen.

Har ila yau shugaban Iran din yace kasarsa na goyan bayan Labanon dari bisa dari kan rashin jituwarta na Isra'ila