Shugaba Ahmadinejad na ziyara a Lebanon

Dubban 'yan kasar Labanon yawancin su magoya bayan Hezbollah ne sukai dafi fi domin tarbar shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmadinejad, yayin da ya kai wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu Beruit, ziyarar da ta jawo suka ciki da wajen Labanon.

Shugaba Ahmadinejad ya ce kasarsa na goyon bayan Lebanon a kan abinda ya kira hare hare daga Isra'ila.

Haka kuma ya ce Iran na goyon bayan wata kasar Lebanon mai karfi da hadin kai a wani kalamin da wata alama ce dake da aniyar kwantar da shakkun cewar ziyarar tasa za ta iya kawo cikas ga yar lumanar siyasar kasar.

Yana magana ne ne dai jim kadan a kudancin Beirut yankin da kungiyar Hezbollah -- kungiyar yan shi'ar da Iran ke goyon baya -- take da karfi.

Ziyarar Ahmadinejad Labanon dai ta nuna karara irin banbance banbancen hauloli da ake da su a kasar, inda wasu ke fargabar na iya jawo rikici a siyasar kasar da ke da rauni.