An kara tsaurara matakan tsaro a Maiduguri

Boko Haram
Image caption Wata caji ofis da 'yan bindiga suka kona a Maiduguri

Hukumomin tsaro a Jihar Borno da ke arewacin Najeriya sun kara tsaurara matakan tsaro a Maiduguri babban birnin jihar.

Hakan ya biyo bayan yawan hare-hare da kashe-kashen da wasu yan bindiga suka shafe kusan watanni uku suna yi kan jami'an yansanda da masu ungwanni har ma da wasu malaman addinin musulunc da kuma jami'an gwamnati.

Jami'an tsaron sun bayyana haka ne a wajen wani taron manema labarai da suka kira yau a Maiduguri, wanda Mataimakin Sufeton Yansanda na Kasa mai lura da shiyya ta 12, A.I.G Mohammed Hadi Zarewa ya jagoranta.

Jam'in tsaron sun yi zargin 'ya'yan Kungiyar nan ta Boko Haram da kai wadannan hare-hare da suka bayyana na sari ka noke ne tun a watannin baya.

A halin da ake ciki kuma wani dan kungiyar ta Boko Haram, Mai suna Malam Ali, wanda duk da yake bai bayyana mana inda yake ba, ya tabbatar mana da cewa dukkan hare haren da ake zargin cewa sune ke kai su ne suka kai su.

Ya bayyana cewar muddun Gwamnati na son sasantawa da su, to kuwa dole su amince da wasu sharudda 5 da suka hada da barin yan kungiyar su wataya, da sakin yan kungiyar dake tsare a gidajen yari ba tare da shari'a ba, kamar yadda ya ce, da kuma dakatar da kisan yan kungiyar da jami'an yansanda ke yi ba trea da wata shara'a ba.