An sabunta: 13 ga Oktoba, 2010 - An wallafa a 16:35 GMT

Ra'ayi Riga: Sha da fataucin miyagun kwayoyi a Yammacin Afrika

Miyagun kwayoyi

Matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi ta zamo ruwan dare a wasu kasashen Afrika

Matsalar fataucin miyagun kwayoyi da kuma shansu matsalace da ta addabi kasashen yammacin Afrika da dama.

Wannan matsalar na daga cikin batutuwan da wasu manyan jami'ai na kungiyar Ecowas ke tattaunawa a kai a birnin Accra na kasar Ghana.

Yaya matsalar fatauci da shan miyagun kwayoyin take a yankunan ku? kuma ta yaya za a shawo kanta?

Akan haka ne za mu tattauna a filin Ra'ayi Riga na wannan makon.

To domin shiga cikin shirin sai ku aiko mana da ra'ayinku a takaice, da kuma lambar wayarku a adireshinmu na e-mail: watau hausa@bbc.co.uk.

Ko kuma ta lambar wayar da aka saba, 44 77 86 20 20 09, ko ta dandalinmu na musayar ra'ayi da muhawara, BBC Hausa Facebook, wanda za ku iya samu a shafinmu na intanet, a BBC Hausa.com.

Ko kuma ta hanyar cike wannan gurbin.

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.