Rundunar sojin saman Burtaniya ta yi gargadi

Jiragen yakin Burtaniya kirar Typhoon
Image caption Jiragen yakin Burtaniya kirar Typhoon

Wani babban jami'in rundunar sojin sama ta Burtaniya ya yi gargadin cewa rage yawan jiragen saman rundunar zai iya raunana tsaron kasar.

Ana dai tunanin cewa, a wani bangare na rage yawan kudin da ta ke kashewa, rundunar sojin saman ta Burtaniya za ta rage da dama daga cikin jiragen yakin da ta mallaka kirar Tornado da Typhoon.

Yayin da ya ke jawabi kafin taron karshe na Majalisar Tsaron Kasa ta Firayim Ministan Burtaniya, shugaban hukumar kula da jiragen yaki, Air Marshal Timo Anderson, ya ce jiragen saman kirar Tornado da Typhoon suna da matukar muhimmanci, ko da kuwa me masu suka za su fada a kansu.

Kwanan nan ne dai aka ambato Firayim Minista David Cameron yana cewa bai dace rundunar sojin saman kasar ta mallaki jiragen da aka tanada don yakar rundunar sojin saman Tarayyar Soviet ba.

Shugaban hukumar kula da jiragen yakin ya shaidawa 'yan majalisar dokokin Burtaniyar cewa idan kasar ta rasa irin wadannan jiragen to ba za ta iya tabbatar da tsaron sararin samaniyar ta ba, kuma ba za ta iya daukar mataki ba idan aka kai mata hari irin wanda aka kai Amurka ranar sha daya ga watan Satumban 2001.

Ya kuma ce rundunar sojin saman ba ta cika lashe kudaden gwamnati kamar rundunar sojin kasa ba.

Rundunonin sojin Burtaniyar biyu dai—ta sama da ta kasa—sun sha kai ruwa rana a daidai lokacin da ake shirin sake nazari a kan kudaden da gwamnati ke kashewa a kan harkar tsaro yayin da alamu ke nuna cewa ba za a rage yawan sojojin kasa ba.

A makon gobe ne dai ake sa ran gwamnati za ta fitar da rahoton irin sauye-sauyen da za ta yi a fannin tsaron kasar.