Najeriya: Majalisar Dattawa ta zargi INEC

Shugaban hukumar zabe a Najeriya, Farfesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban hukumar zabe a Najeriya, Farfesa Attahiru Jega

Majalisar Dattawa a Najeriya ta zargi Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, da yunkurin shafa mata kashin kaji.

Majalisar ta ce hukumar ta boye gazarwar ta wajen shirye-shiryen zaben da za a gudanar a shekarar 2011.

Gagarabadan majalisar, Sanata Kanti Bello, ya shaidawa BBC cewa shugaban hukumar zaben, Farfesa Attahiru Jega, yana yiwa ’yan majalisar barazana.

“Duk lokacin da aka tashi sai ya zo kamar yana yi mana barazana.

“Da farko... ya ce zai iya gudanar da zaben cikin watan Janairu, ya gaya mana in an taimake shi an ba shi kudi miliyan dubu hamsin da biyar in zai sayo abubuwan nan da kan shi, muka ce a ba shi; ya kuma ce in sai ya ba da kwangila yana son miliyan dubu saba’in da hudu, muka yarda; maimakon ma ya nemi hakan ya ce miliyan dubu tamanin da tara: muna hutu muka yanke hutun mu muka dawo don dai kada a ce ga wani laifin da muka yi.

“Ya tafi a kan an ba shi komai [sai] kwatsam ya komo ya ce yanzu bai iya gudanarwa....

“Shin don Allah don Annabi menene dalilin shi da zai rika wannan ban-tsoro?

“In ya san ba zai iya yin zaben nan ba, don Allah ka da ya goga mana, muna da mutunci”.

Majalisar ta kuma nemi kwamitinta dake sa ido a kan harkokin zabe ya ziyarci shugaban hukumar zaben don gargadinsa a kan yawan korafe-korafen da hukumar ke yi.

Sai dai kuma hukumar zaben ta ce tana yawan korafin ne don ganin cewa an gudanar da zabe mai inganci a shekara mai zuwa.

Kakakin hukumar, Nick Dazang, ya bayyanawa BBC cewa:

“Shi dai [Farfesa Attahiru Jega] ya nuna ne cewa idan da za a yi sauye-sauyen nan cikin lokaci hukumar zabe za ta samu isasshen lokaci kuma ta yi aiki mai inganci”.

Mista Dazang ya kuma musanta cewa hukumar zaben na kokarin shafawa Majalisar Dattawan kashin kaji.