An kashe dan sanda a Bauchi

Wani ofishin 'yansanda da a ka kon a Najeriya
Image caption An halaka wani dan sanda a jihar Bauchi

Rundunar 'yansanda ta jihar Bauchi da ke Najeriya ta ce, wasu mutane da ba a san ko su waye ba, sun halaka wani dan sanda a jihar.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Danlami 'Yar aduwa ya tabbatarwa da BBC cewa wadansu mutane ne da ke kan babur su ka halaka dan sandan, a kofar gidan da ya ke gadi.

Sai dai bai yi karin bayani ba, inda ya ce har yanzu suna bincike kan lamarin.

Wannan lamari dai ya faru ne ranar laraba da almuru a Unguwar Zango da ke garin na Bauchi.

Kisan dan sandan ya sanya fargaba ga al'umar garin kasancewa irin wannan kisa, da a ke zargin 'yan kungiyar Boko Haram da aikatawa na faruwa a jihar Borno da ke makotaka da jihar Bauchin.