An kammala ceto mahaka ma'adanai a Chile

Mutumin karshe da aka fito da shi daga ramin  karkashin kasa
Image caption An kammala aikin ceto a kasar Chile

An yi ta murna a kasar Chile, a wurin mahakar ma'adanan da aka kammala ceto mutane talatin da uku, wadanda wani ramin hakar ma'adanai ya rufta musu fiye da watanni biyu da suka gabata.

Shugaban kasar, Sebastian Pinera ya ce, yanzu kasar ta sauya matuka sakamakon nasarar ceto mahaka ma'adanan.

Mista Pinera ya kara da cewa zai tabbatar an dauki kwararan matakai wajen kare mahaka ma'adanan kasar.

Jama'a sun yi ta sowa a lokacin da a ka fito da mutum na karshe zuwa doron kasa.

'Yan kasar ta Chile za su dade basu manta da abubuwan da su ka faru cikin fiye da watannni biyun da suka gabata, musamman jajircewar da a ka yi wajen ceto mahaka ma'adinan.