Kanal Abdullahi Badie yana gidansa a yanzu

Tutar Niger
Image caption Kanal Abdullahi Badie na gidansa

Wasu rahotanni daga Jumhuriyar Nijer sun nuna cewa tsohon Sakataren majalisar koli ta mulkin sojan kasar, CSRD, Kanal Abdullahi Badie, yanzu haka yana gidansa, bayanda tun farko aka bada rahoton cewa hukumomin mulkin sojan kasar sun kama shi tare da wasu hafsoshin soja bisa zargin kulla makarkashiyar kifar da gwamnati. Sauran wadanda aka ce an kaman sun hada da tsohon Kwamandan zaratan sojoji na Guarde Nationale ko National Guard, Kanal Abdu Sidiku Isa da kuma ministan Ayyuka, Kanal Amadu Diallo.

Jama'a da kungiyoyin farar hula dai a Jumhuriyar ta Nijer na cigaba da bayyana damuwarsu dangane da rahotannin kama hafsoshin sojan da aka ce majalisar koli ta mulkin soja ta CSRD ta yi.

Kungiyoyin musamman, na nuna damuwa ne cewa irin wannan hali zai iya jefa shirin da ake yi na mayar da kasar bisa tafarkin Demokradiyya, cikin wani rashin tabbas.