Dan takarar AC ne ya lashe zaben Ekiti: Kotu

Dr Kayode Fayem
Image caption Mutumin da kotu tace shi ne zababben gwamnan jihar Ekiti

A Najeriya wata babbar kotun daukaka kara ta tabbatar da Dr Kayode Fayemi dan takarar gwamna na jam'iyyar Action Congress -AC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Ekiti.

Kotun ta ce bayan ta yi nazari kan sakamakon zaben da aka sake gudanarwa a bara, bayanai sun nuna cewa Dr Fayemi ne ya lashe zaben, ba Segun Oni na jam'iyyar PDP ba.

Wannan hukuncin dai ya zo ne bayan wata kotun sauraron kararrakin zaben a baya ta tabbatar da cewa Mr. Segun Oni na jam'iyyar PDP ne ya ci zaben.

Tun bayan zaben shekara ta 2007 ne, jam'iyyar ta AC ta garzaya kotu tana kalubalantar zaben na Segun Oni, inda kotu ta umarci a sake gudanar da zabe a wasu mazabu a jihar.

Amma bayan sake zaben sai aka kara bayyana jam'iyyar PDP a matsayin wacce ta lashe zaben. Abin da yasa Fayemi ya kara garzayawa kotu.

Masu lura da al'amura na ganin hukuncin kotun zai iya yin tasiri sosai ganin irin mahimmancin da jihar ke da shi a siyasance a yankin kudu maso yammacin Najeriya.