An magance matsalar cutar dabbobi

Tambarin hukumar Abinci Ta Duniya
Image caption An magance cutar dabbobi

An kawo karshen wani yunkuri da kasashen duniya ke yi na kawar da cutar dabbobin da ta addabi wasu dabbobi a nahiyar Afrika da Asiya da kuma kasashen Turai a shekarun baya.

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, za ta dakatar da duk wasu aikace-aikace na yaki da cutar, wanda hakan ke sanar da kawo karshen yaki da ita.

Hukumar ta ce wannan ne karon farko da dan Adam ya yi nasarar kawar da wata cutar dabbobi a duniya.

Alamomin cutar dai sun hada da kirci,da kuma kumfar baki daga wajen dabbobi.