Majalissar dattawa ta ja kunne Professor Jega

Prof Attahiru Jega
Image caption Prof Attahiru Jega

Kwamitin da'a na majalissar dattawan Nigeria ya nemi shugaban hukumar zabe ta kasa, Professsor Attahiru Jega, da ya daina yawan maganganu, musamman tare da 'yan jarida.

Kwamitin ya bayyana haka ne a yayin da ya gana da shugaban hukumar zaben domin bincike akan kalaman da ake zargin yayi na dorawa yan majalissar dattawan laifin kawo jinkiri wajen amincewa da sabuwar dokar zabe.

Kwamitin ya ce a madadin yawan maganganu kamata yayi shugaban hukumar zaben ya maida hankali wajen tabbatar da an gudanar da zabe ingantacce.

Wasu wakilan kwamitin sun musanta cewa yin hakan tamkar tauyewa Professor Jega hakkinsa ne na bayyana albarkacin bakinsa akan duk wani abu da ya ga baya tafiya daidai.jega