Kamfanoni na gurbata muhalli a Nijar

Tutar jamhuriyar Nijar
Image caption Kamfanoni na gurbata muhalli a Nijar

A jamhuriyar Nijar, kungiyar GREN mai fafutukar ganin 'yan kasar sun ci moriyar arzikin ma'adanan da Allah ya hore wa kasar, ta zargi kamfanonin kasar Sin masu hako man fetur a Nijar da gurbata muhalli.

Kungiyar ta ce, wani bincike da ta gudanar ya tabbatar mata da cewa ayyukan da kamfanonin ke yi sun shafi gonakin manoma da dama, kuma akwai bukatar a biya su diya.

A shekara ta 2009 ne dai kamfanin kasar Sin ya soma ayyukan tono man fetur a yankin Agadem da ke cikin jahar Diffa da zummar fito da gangar mai ta farko a shekara ta 2012.

Matatar man kuma na iya samar da gangar mai dubu ashirin a kowace rana, wanda a ka ce zai ishi 'yan kasar har ma a sayar wa kasashen waje.