Ra'ayi Riga: Me ke kawo matsalar shan miyagun kwayoyi?

Cocaine
Image caption Cocaine

Sha da fataucin miyagun kwayoyi wata matsala ce da yanzu kusan ta zama ruwan dare a kasashe daban-daban na duniya.

Hakan ya sa ofishin majalisar dinkin duniya kan laifuka da fataucin miyagun kwayoyi, tare da sauran kasashen duniya suna yunkurin kaddamar da wani shiri na musamman domin samun hadin kai tsakanin kasashen Afrika guda bakwai da kuma kasar Brazil domin gano yadda za a fuskanci wannan matsala.

Hukumar ta majalisar dinkin duniya ta ce an yi fataucin kimanin tan talatin zuwa dari na hodar iblis ta "Cocaine" zuwa yammacin Afrika a shekarar da ta gabata. Wani abu dake jan hankali shi ne matasa su suka fi tsunduma cikin wannan harka.

To domin tattauna wannan batu mun gayyato baki daban-daban da suka hada da ;Shuagaban hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya - NDLEA, Alhaji Ahmadu Gyade, da Alhaji Baba Hussein, Darektan gudanarwa na hukumar ta NDLEA dake halartar taron da kungiyar Ecowas ta shirya a Ghana.

Akwai kuma Dan majalisar wakilai ta Najeriya, Rabe Nasiru da kuma Chief Umaru Baba Issah, shugaban wata kungiya mai zaman kanta ta Muslim Family Counselling wacce ke kokarin yaki da shan miyagun kwayoyi.

Akwai kuma wasu daga cikinku, ku masu saurarenmu, wadanda suka bayyana ra'ayoyinsu ta kan layin tarho.