An gina hanyar karkashin kasa a Switzerland

Hanyar karkashin kasa
Image caption Hanyar karkashin kasa

A Switzerland, masu aikin gina da kuma manyan jami'ai sun yi ta shewa don murna, yayin da wani makeken injin ya huda sauran mitocin da suka rage, na wani dutse da ke karkashin tsaunukan Alps, domin kammala ginin hanyar karkashin kasa mafi girma a duniya.

An kwashe shekaru goma sha hudu ana ginin hanyar karkashin kasar, mai tsawon kilomita hamsin da bakwai, kuma an kashe dala biliyan goma:

Darektan ma'aikatar sufurin Switzerland ya ce, kasar na son hanyoyin karkashin kasa ainun. Shekaru dari kenan muna gina hanyoyin karkashin kasa.

Jirage masu gudun gaske ne zasu rika zirga-zirga tsakanin arewaci da kudancin Turai, yayin da aka bude hanyar nan da shekaru bakwai masu zuwa.

Za a kuma sami saukin cunkoso da kuma gurbatar muhalli a kan hanyoyin da ke doron kasa, a wannan yanki na tsaunukan Alp na Switzerland.